Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Tarayya za ta kwaso sama da ’yan Najeriya 742 daga Afirka...

Gwamnatin Tarayya za ta kwaso sama da ’yan Najeriya 742 daga Afirka ta Kudu

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta kwashe sama da ’yan Najeriya 742 da ke ƙasar Afirka ta Kudu kafin ranar 30 ga Yuni, sakamakon hare-haren kyamar baƙi da ke ci gaba da ƙaruwa a ƙasar.  

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta kwashe sama da ’yan Najeriya 742 da ke ƙasar Afirka ta Kudu kafin ranar 30 ga Yuni, sakamakon hare-haren kyamar baƙi da ke ci gaba da ƙaruwa a ƙasar.  

Ministar Harkokin Waje, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu, ta ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta himmatu wajen tabbatar da cewa babu wani ɗan Najeriya da ya nemi komawa gida da za a bari a baya.  

Ta bayyana cewa an riga an kwaso rukuni na farko da ya ƙunshi mutum 258, yayin da kusan mutum 1,000 suka yi rajistar komawa Najeriya. Ana sa ran za a kwaso sauran fiye da mutum 742 cikin kwanaki masu zuwa kafin wa’adin ranar 30 ga Yuni.  

Ministar ta kuma nuna damuwa kan hare-haren da ake kai wa ’yan Najeriya da sauran baƙin haure a Afirka ta Kudu, tana mai cewa gwamnati na ci gaba da tattaunawa da hukumomin ƙasar domin kare rayuka da haƙƙin ’yan Najeriya.

SourceVanguard
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments