Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiMahara sun hallaka jami’an sa-kai biyu a sabon hari da suka kai...

Mahara sun hallaka jami’an sa-kai biyu a sabon hari da suka kai Jihar Filato

Wasu da ake zargin masu ɗauke da makamai ne sun kashe jami’an sa-kai biyu a wani hari da suka kai kauyen Rangarasa da ke yankin Rantya, Ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato.

Wasu da ake zargin masu ɗauke da makamai ne sun kashe jami’an sa-kai biyu a wani hari da suka kai kauyen Rangarasa da ke yankin Rantya, Ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato.

Rahotanni sun ce maharan, waɗanda adadinsu ya haura 100, sun kutsa cikin yankin ne a kan babura tare da harbe-harbe domin shiga cikin al’umma. Sai dai jami’an sa-kai sun yi ƙoƙarin tare su, amma sun fi ƙarfinsu da makamai.  

An bayyana sunayen jami’an sa-kan da suka rasu da Joshua da Emmanuel. Wani mazaunin yankin ya ce jami’an tsaro sun isa wurin ne da safe bayan harin ya ƙare.  

Shugaban Ƙungiyar Matasan Berom BYM, Barrista Dalyop Solomon Mwantiri, ya nuna damuwa kan ƙaruwar hare-haren da ke ƙara matsowa kusa da tsakiyar birnin Jos, tare da kira ga gwamnati da hukumomin tsaro su ɗauki matakan gaggawa domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.  

SourceVanguard
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments