Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeItaliya za ta sake buɗe ofishin jakadancinta a Tehran ranar Juma’a

Italiya za ta sake buɗe ofishin jakadancinta a Tehran ranar Juma’a

Ministan Harkokin Wajen Italiya, Antonio Tajani, ya sanar a ranar Laraba cewa ƙasar za ta sake buɗe ofishin jakadancinta da ke Tehran, babban birnin Iran, a ranar Juma’a.

Ministan Harkokin Wajen Italiya, Antonio Tajani, ya sanar a ranar Laraba cewa ƙasar za ta sake buɗe ofishin jakadancinta da ke Tehran, babban birnin Iran, a ranar Juma’a.

Ya bayyana hakan ne yayin zaman tambayoyi a majalisar dokokin ƙasar, inda ya ce jakadan Italiya da sauran jami’an ma’aikatar harkokin wajen ƙasar za su koma Tehran domin ci gaba da ayyukansu.

Tun da farko Italiya ta rufe ofishin jakadancin nata saboda tashin hankalin da ya dabaibaye yankin Gabas ta Tsakiya.

Tajani ya bayyana yarjejeniyar fahimtar juna da aka cimma tsakanin Amurka da Iran a matsayin wani abin ƙarfafa gwiwa da ke nuna yiwuwar samun zaman lafiya a yankin.

Ya kuma ce zai tattauna da Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, yana mai jaddada cewa Italiya a shirye take ta tallafa wajen tabbatar da cewa yarjejeniyar ta kai ga zaman lafiya mai ɗorewa.

Ministan ya kuma jaddada muhimmancin tabbatar da zirga-zirgar jiragen ruwa cikin ’yanci a mashigar Hormuz, yana mai cewa hakan na da matuƙar muhimmanci ga tattalin arzikin Italiya.

Rahotanni sun nuna cewa Amurka da Iran sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta wucin gadi a watan Afrilu ta hanyar shiga tsakani da Pakistan, sannan a ranar Litinin suka sanar da wata yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin, wadda ake sa ran za a sanya wa hannu a hukumance ranar Juma’a a ƙasar Switzerland.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments