Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da FreeTV, sabon talabijin da zai bai wa ’yan Najeriya damar kallon tashoshi sama da 100 ba tare da biyan kuɗin wata-wata ba.
Dandalin zai haɗa da tashoshin labarai, wasanni, fina-finai, kiɗa, ilimi, yara da kuma shirye-shirye cikin Hausa, Yarbanci da Igbo.
An ce za a iya amfani da FreeTV ta tauraron ɗan adam, tsarin watsa shirye-shiryen ƙasa da kuma manhajar wayar hannu, ba tare da sai an sayi sabon talabijin ba idan na’urar tana da tsarin DVB-T2 ko DVB-S2.