Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiYan sanda sun cafke wata matashiya kan zargin kashe kakarta a Katsina

Yan sanda sun cafke wata matashiya kan zargin kashe kakarta a Katsina

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina ta kama wata budurwa mai shekaru 20, Aisha Muktar Hassan, bisa zargin hallaka kakarta mai shekaru 97, Hajiya Ummukhulsum Hassan, a garin Daura.

Rahotanni sun ce rikici ya ɓarke tsakaninsu, inda ake zargin Aisha ta bugi kakarta da kujera a kai.

Jami’an ’yan sanda sun isa wurin bayan samun rahoto, suka tarar da tsohuwar cikin mawuyacin hali tana zubar da jini.

An garzaya da ita asibiti, amma likitoci sun tabbatar da rasuwarta.

Rundunar ta ce ana ci gaba da bincike, kuma za a gurfanar da wadda ake zargi a gaban kotu bayan kammala bincike.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments