Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da talabijin ta zamani 'dijital', tana sa ran...

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da talabijin ta zamani ‘dijital’, tana sa ran kai wa gidaje miliyan 40

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin Digital Switch Over, DSO, wanda zai sauya tsarin watsa shirye-shiryen talabijin daga tsohon tsarin analog zuwa na dijital, tare da burin kai wa gidaje miliyan 40 a faɗin Najeriya.

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin Digital Switch Over, DSO, wanda zai sauya tsarin watsa shirye-shiryen talabijin daga tsohon tsarin analog zuwa na dijital, tare da burin kai wa gidaje miliyan 40 a faɗin Najeriya.

An ƙaddamar da shirin ne a Abuja, inda Ministan Sadarwa, Ƙirkire-ƙirkire da Tattalin Arzikin Zamani, Bosun Tijani, ya bayyana cewa wannan wani muhimmin mataki ne a sauyin fasahar zamani a ƙasar, wanda zai iya samar da damarmakin tattalin arziki da ya haura Naira biliyan 600.

Ya ce shirin zai inganta samun bayanai, ilimi da shirye-shiryen al’adu, musamman ga al’ummomin karkara da ba su da isasshen damar samun irin waɗannan ayyuka.

Darakta Janar na Hukumar NBC, Charles Ebuebu, ya ce shirin ba na watsa shirye-shirye kaɗai ba ne, domin zai buɗe ƙofofin ayyukan yi da kasuwanci ga masu ƙirƙirar abun ciki, gidajen watsa labarai da masu zuba jari.

Haka kuma, shugabar NigComSat Ltd, Jane Egerton-Idehen, ta ce sabon tsarin zai samar da ƙarin ayyukan yi, inganta harkar talla tare da ba masu kallo ingantaccen hoto, sauti mai kyau da ƙarin zaɓin tashoshin talabijin.

Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa cikakken aiwatar da tsarin zai ƙarfafa masana’antar cikin gida, bunƙasa samar da shirye-shirye da kuma samar da sabbin hanyoyin samun kuɗaɗen shiga ga kafafen yaɗa labarai.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments