Gwamnatin Equatorial Guinea ta yi murabus bayan ta gaza cimma muhimman manufofin aikin da aka gindaya mata, a cewar mataimakin shugaban ƙasar.
Mataimakin shugaban ƙasar kuma ɗan shugaban ƙasa, Teodoro Nguema Obiang Mangue, ya bayyana a shafinsa na X cewa firaministan ƙasar ya miƙa takardar murabus ɗin gwamnati saboda ta samu nasarar cika kusan kashi 10% kacal na manufofin da aka sa mata.
Sai dai bai bayyana irin manufofin da ake sa ran gwamnati ta cimma ba. Wata sanarwa daga jam’iyyar da ke mulki ta ce shugaban ƙasar ya lura cewa gwamnati ta gaza yaƙi da cin hanci da rashawa tare da kasa bunƙasa tattalin arzikin ƙasar ta hanyoyi daban-daban.
Mataimakin shugaban ƙasar ya ce murabus ɗin ya yi daidai da ƙa’idar cewa dole ne gudanar da harkokin gwamnati ya kasance tare da samar da sakamako mai kyau.