Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Kano ta yi gargaɗi kan sayar da jabun kaya a kasuwanni

Gwamnatin Kano ta yi gargaɗi kan sayar da jabun kaya a kasuwanni

Gwamnatin Jihar Kano ta ja hankalin ’yan kasuwa, kamfanoni da masu rarraba kayayyaki kan gujewa sayar da jabun kaya ko waɗanda ba su da inganci a kasuwanni.

Hakan na ƙunshe a cikin wata sanarwa da Daraktan Wayar da Kai na Hukumar Kare Haƙƙin Masu Sayen Kaya ta jihar, Malam Jamilu Mustapha Yakasai, ya fitar a ranar Laraba, 17 ga Yuni, 2026.

Sanarwar ta bayyana cewa Shugaban hukumar, Dakta Ibrahim Garba Muhammad, ya tabbatar da cewa gwamnati na ƙara ƙaimi wajen tabbatar da cewa ana sayar da kayayyaki masu inganci da amintattu a faɗin jihar.

Ya kuma shawarci jama’a da su rika duba muhimman bayanai kamar ranar karewa, sunan masana’anta da sauran ƙa’idoji kafin saye ko amfani da kaya.

Haka kuma, ya ce hukumar na ci gaba da kai farmaki kasuwanni da shaguna domin gano jabun kaya tare da tabbatar da bin doka.

Sanarwar ta ƙara da cewa ana kira da jama’a su rika kai rahoton duk wani abu da suka lura da shi na karya doka, tare da tabbatar da kariyar bayanan masu kai rahoton.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments