Ministan harkokin wajen ƙasar Rasha,
Sergei Lavrov, ya yi kira ga Israel da ta mutunta yarjejeniyar fahimta da aka cimma tsakanin Iran da Amurka, yana mai jaddada bukatar rage tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya.
Lavrov ya bayyana cewa Rasha na goyon bayan duk wani mataki da zai taimaka wajen kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali, tare da kira ga dukkan ɓangarori su cika alkawuran da aka amince da su a yarjejeniyar.
Ya kuma ce bai dace wasu ƙasashe su bi ƙa’idoji yayin da wasu ke yin watsi da su ba, yana mai cewa hakan na iya ƙara dagula rikici a yankin.
Wannan matsaya ta Rasha na zuwa ne a daidai lokacin da Israel ke ci gaba da kai hare-hare a kudancin Lebanon, yayin da Iran ke nuna cewa dakatar da rikicin Lebanon na daga cikin muhimman abubuwan da yarjejeniyar fahimtar ta ƙunsa.