Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiTrump ya ci amanar mu – Jami’an tsaron Isra’ila

Trump ya ci amanar mu – Jami’an tsaron Isra’ila

Wasu manyan jami’an Isra’ila sun nuna rashin jin daɗinsu kan wata yarjejeniya da ake zargin tana kunno kai tsakanin Amurka da Iran, suna masu cewa ba ta magance manyan barazanar da ke tattare da shirye-shiryen nukiliya da makamai masu linzami na Iran ba.

Rahotanni daga kafar yaɗa labarai ta Ynet ta Isra’ila sun bayyana cewa wasu jami’an gwamnatin ƙasar sun yi zargin cewa yarjejeniyar na iya cutar da muradun tsaron Isra’ila, tare da nuna damuwa cewa ba a yi la’akari da ra’ayoyinsu yadda ya kamata ba yayin tattaunawar.

A cewar rahoton, wasu daga cikin jami’an sun bayyana cewa yarjejeniyar da ake tattaunawa a kai ba ta bayar da isassun matakan da za su hana Iran ci gaba da wasu ayyukan da Isra’ila ke kallon a matsayin barazana ga tsaron yankin Gabas ta Tsakiya.

Wani babban jami’in Isra’ila da ba a bayyana sunansa ba ya bayyana cewa shugaban Amurka, Donald Trump, ya ci amanar Isra’ila ta hanyar amincewa da tsarin yarjejeniyar da ba ya kare bukatun ƙasar yadda ya kamata.

Sai dai har zuwa yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga Fadar White House ko gwamnatin Iran da ta yi tsokaci kai tsaye kan waɗannan zarge-zargen.

Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan makomar dangantaka tsakanin Amurka da Iran, yayin da kasashen duniya ke sa ido kan duk wani mataki da ka iya tasiri ga tsaro da zaman lafiyar yankin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments