Wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun ƙone makarantun firamare da sakandare da ke ƙauyen Kautikari a Ƙaramar Hukumar Chibok ta Jihar Borno.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kai farmakin ne da misalin ƙarfe 7:00 na yammacin ranar Asabar, inda suka banka wa makarantun wuta tare da haddasa asarar dukiyoyi.
Lamarin ya faru ne kasa da wata guda bayan sace wasu ɗalibai daga makarantar Firamare da Sakandare ta Mussa da ke Ƙaramar Hukumar Askira-Uba, lamarin da har yanzu ba a gano inda ɗaliban suke ba.
Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa duk da barnar da aka yi wa makarantun, babu rahoton rasa rai a harin.
Sai dai mazauna yankin sun tsere zuwa dazuka da sauran wurare domin neman mafaka yayin da maharan suka mamaye garin.
Wani mazaunin yankin ya ce wannan ba shi ne karo na farko da ƙauyen Kautikari ke fuskantar hari daga ’yan ta’adda ba, domin sun sha kai hare-hare a yankin a baya.
Sai dai a wasu hare-haren da suka gabata, ba a samu lalata kadarorin gwamnati ko na jama’a kamar yadda aka gani a wannan karon ba.
Harin ya sake nuna irin ƙalubalen tsaro da ke ci gaba da addabar wasu sassan Jihar Borno duk da ƙoƙarin hukumomi na daƙile ayyukan ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.