Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya bukaci al’ummar Musulmi a Najeriya su fara neman ganin jinjirin watan Muharram 1448AH domin tantance farkon sabuwar shekarar Musulunci.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban Kwamitin Ba da Shawara kan Harkokin Addini na Majalisar Masarautar Sokoto, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ya sanya wa hannu.
Sanarwar ta bayyana cewa ranar Litinin, 15 ga Yunin 2026, wadda ta yi daidai da 29 ga watan Zulhijjah 1447AH, ita ce ranar da aka ware domin sa ido kan jinjirin watan a dukkan sassan Najeriya.
Sarkin Musulmin ya bukaci Musulmai su rika kallon sararin sama bayan faduwar rana, sannan su kai rahoton duk wani sahihin gani ga hakimai ko shugabannin al’ummominsu domin a isar da bayanin ga Majalisar Masarautar Sokoto.
A cewarsa, aikin neman jinjiri wata muhimmiyar ibada ce da ake gudanarwa duk shekara domin tabbatar da fara sabbin watannin Musulunci.
Watan Muharram na daga cikin watanni huɗu masu alfarma a Musulunci, kuma shi ne watan farko a kalandar Musulunci.
Haka kuma, sakamakon ganin jinjirin ne zai tabbatar da ranar da za a fara sabuwar shekarar Hijira ta 1448AH ga Musulman Najeriya.