Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiSERAP ta maka NNPCL kotu kan N5.9bn da ta kashe wajen sauya...

SERAP ta maka NNPCL kotu kan N5.9bn da ta kashe wajen sauya suna

Kungiyar kare hakkin jama’a ta SERAP ta kai karar Kamfanin Mai na Najeriya NNPCL kotu domin neman karin haske kan yadda aka kashe kusan Naira biliyan 5.9 wajen sauya tsohon sunan NNPC zuwa NNPCL.

Kungiyar ta bukaci kotu ta umarci kamfanin da ya fitar da cikakken bayani kan yadda aka kashe kudaden, sunayen kamfanonin da suka gudanar da aikin sauya sunan, da kuma jami’an da suka amince da kashe kudin.

SERAP ta kuma nemi a bayyana ko an bi dokoki da ka’idojin gwamnati wajen bayar da kwangilolin da suka shafi aikin.

A cewarta, jama’a na da hakkin sanin yadda ake amfani da kudaden gwamnati.

Kungiyar ta kara da cewa a baya Majalisar Dattawa ta nuna damuwa kan wannan kashe kudi, amma har yanzu ba a sanya ranar fara sauraron karar ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments