Saturday, October 17, 2026
HomeTsaroMutumin da ake zargi da tunzura sojoji su kifar da gwamnatin Tinubu...

Mutumin da ake zargi da tunzura sojoji su kifar da gwamnatin Tinubu ya gurfana a gaban kotu

Paul Jibrin Oweleke ya musanta dukkanin zargin da hukumar DSS ke yi masa

Hukumar DSS ta gurfanar da wani mutum mai suna Paul Jibrin Oweleke a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke jihar Legas a ranar Litinin bisa zargin amfani da kafafen sada zumunta wajen kiran a yi juyin mulki domin kifar da Shugaba Bola Tinubu daga mulki.

An gurfanar da Oweleke ne kan tuhumar laifuka biyu na amfani da yanar gizo ba bisa ka’ida ba da kuma watsa saƙonni da ake zargin za su iya tayar da hankalin jama’a.

DSS ta ce ya yi amfani da shafinsa na sada zumunta mai suna “Oweleke TV” wajen wallafa saƙonni da ake zargin suna kiran sojoji su kifar da gwamnati, tare da kwaikwayon abin da ya faru a ƙasar Burkina Faso.

Masu gabatar da ƙara sun ce waɗannan saƙonni na da nufin tayar da rikici, haifar da rashin jituwa, da kuma dagula zaman lafiya a ƙasar

A yayin zaman kotu, lauyan DSS ya bayyana cewa wanda ake tuhuma ya kuma yi amfani da wannan shafi wajen yin barazana ga Shugaba Tinubu.

DSS ta ce laifukan da ake tuhumar sa da su sun saba da tanadin Sashe na 24(1)(b) da 24(2)(a) na Dokar Laifukan Yanar Gizo ta 2015, wadda aka yi gyara a 2024.

Lauyan wanda ake tuhuma ya shigar da bukatar belinsa, yayin da mai gabatar da ƙara ya ce yana bukatar lokaci domin duba takardun.

Mai shari’a Akintoye Aluko ya dage shari’ar zuwa 16 ga Yuni, 2026 domin sauraron bukatar beli, sannan ya umarci a ci gaba da tsare wanda ake tuhuma a gidan yari har sai an kammala batun belin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments