Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaADC ta fara zawarcin Gawuna don zama dan takarar Gwamnan Kano a...

ADC ta fara zawarcin Gawuna don zama dan takarar Gwamnan Kano a 2027

ADC ta yi wa Gawuna tayin tikitin gwamna da goyon bayan yakin neman zabe

Jam’iyyar ADC na kokarin jawo tsohon dan takarar gwamnan Kano, Nasiru Gawuna, domin ya tsaya takarar gwamna a karkashinta a zaben 2027.

Majiyoyi sun bayyana cewa ana ci gaba da tattaunawa tsakanin shugabannin jam’iyyar da makusantan Gawuna, inda aka ce an yi masa tayin tikitin gwamna tare da alkawarin samun cikakken goyon bayan yakin neman zabe.

Rahotanni sun kuma nuna cewa wasu daga cikin magoya bayansa za su iya samun tikitin takarar kujerun majalisar dokokin jihar da ta tarayya idan har ya amince da shiga jam’iyyar.

Duk da cewa Gawuna ya sha bayyana biyayyarsa ga tafiyar Kwankwasiyya, ana rade-radin cewa ADC na ci gaba da matsa masa lamba domin ya sauya sheka kafin zaben 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments