Sunday, October 18, 2026
HomeTsaroBoko Haram ta saki mata da yara 416 da aka yi garkuwa...

Boko Haram ta saki mata da yara 416 da aka yi garkuwa da su a Jihar Borno

Kungiyar Boko Haram ta saki mata da yara 416 da aka yi garkuwa da su daga garin Ngoshe da ke ƙaramar hukumar Gwoza a Jihar Borno, bayan shafe watanni suna tsare a hannunta.

Shugaban ƙungiyar Borno South Youths Alliance (BOSYA), Samaila Kaigama, ya tabbatar da sakin mutanen a ranar 6 ga Yuni, 2026.

Ya ce sakin nasu ya biyo bayan tattaunawa da ƙoƙarin shiga tsakani da wasu shugabannin al’umma suka yi domin ganin an kuɓutar da su.

Tun da fari dai, a ranar 3 ga Maris, 2026, mayaƙan Boko Haram sun kai hari Ngoshe inda suka kai farmaki kan sansanin sojoji, suka kashe mutane da dama tare da yin awon gaba da ɗaruruwan mazauna yankin, galibinsu mata da yara.

Daga baya an tabbatar da cewa mutum 416 ne ke hannun masu garkuwar.

A watan Afrilu, wata ƙungiyar Boko Haram ta fitar da bidiyon waɗanda aka sace, inda aka nuna mata da yara suna roƙon gwamnati da shugabanni su taimaka wajen dawo da su gida.

A lokacin, BOSYA ta bayyana cewa tana shiga tsakani domin neman hanyoyin da za a kuɓutar da su.

Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin waɗanda aka sace sun samu tserewa tun kafin sakin na baya-bayan nan, yayin da sojojin Operation Hadin Kai suka ceto wasu mata da yara shida daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su a watan Mayu.

Sakin mutanen 416 ya kawo ƙarshen watanni na fargaba da damuwa ga iyalansu da al’ummar Ngoshe, waɗanda suka dade suna jiran samun labarin kuɓutar su daga hannun masu tayar da kayar baya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments