Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiWHO da Africa CDC sun ware dala miliyan 518 domin dakile yaduwar...

WHO da Africa CDC sun ware dala miliyan 518 domin dakile yaduwar Ebola a Afirka

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO tare da cibiyar kula da rigakafin cututtuka ta Afirka Africa CDC sun ƙaddamar da wani shiri na dala miliyan 518 domin yaƙi da barkewar cutar Ebola da ke ci gaba da barazana a wasu sassan nahiyar Afirka.

Shirin, wanda zai gudana daga watan Yuni zuwa Nuwamba 2026, zai mayar da hankali kan gano masu ɗauke da cutar cikin gaggawa, ƙarfafa ayyukan jinya da kuma tallafa wa ƙasashen da ke fuskantar haɗarin barkewar Ebola.

Jami’an lafiyar sun bayyana cewa shirin zai taimaka wajen rage yaduwar cutar da kare rayukan al’ummomin da ke cikin haɗari.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments