Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya Abuja ta sanar da kama wani fitaccen mutum da ake nema ruwa a jallo mai suna Yau Sule, wanda ake zargi da samar wa ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane harsasai da sauran kayan aiki.
Kwamishinan ‘Yan Sandan
Abuja, CP Ahmed Mohammed Sanusi, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar an Abuja ranar Juma’a.
A cewarsa, kamen ya biyo bayan wani samame na musamman da jami’an tsaro suka gudanar bisa sahihan bayanan sirri.
Ya ce an dade ana neman Yau Sule tun shekarar 2023 saboda zargin da ake masa na hannu a ayyukan da suka shafi samar da kayan aiki ga kungiyoyin masu aikata laifuka.
CP Sanusi ya bayyana cewa an kama wanda ake zargin ne a ranar 2 ga Yuni, 2026, yayin da yake tafiya a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Ya ce binciken farko ya nuna cewa an samu harsasai masu yawa a hannun wanda ake zargin, ciki har da harsasai 81 na bindigar AK-47 masu tsayin milimita 7.62 da kuma harsasai 100 na bindigar GPMG masu tsayin milimita 7.62.
Kwamishinan ya kara da cewa Yau Sule na cikin mutanen da hukumomin tsaro ke nema a jihohi da dama na Arewa ta Tsakiya bisa zargin alaka da ayyukan ’yan bindiga.