Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiWani mutum ya mutu yayin kokarin ciro wayarsa daga rijiya a Kano

Wani mutum ya mutu yayin kokarin ciro wayarsa daga rijiya a Kano

Rashin iskar oxygen ya hallaka wani mutum a cikin rijiya.

Wani mutum mai suna Yusuf Usman, mai shekaru 45, ya rasa ransa bayan ya shiga wata tsohuwar rijiya da aka daina amfani da ita a garin Kwa da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano domin ciro wayar hannu da ta fada cikinta.

Mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Abdullahi, ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar.

A cewarsa, hukumar ta samu kiran neman agajin gaggawa da misalin karfe 11:13 na safe ranar Laraba, inda aka sanar da ita cewa wani mutum ya makale a cikin wata rijiya a garin Kwa.

Ya bayyana cewa nan take aka tura jami’an ceto zuwa wurin da abin ya faru. Da isarsu, sun tarar da Yusuf Usman a cikin rijiyar bayan ya shiga domin ciro wayarsa da ta fada ciki, amma ya kasa fitowa.

Jami’an sun yi kokarin ceto shi tare da fitar da shi daga rijiyar, amma a lokacin yana cikin ya suma.

Sai dai bayan an ciro shi, an tabbatar da cewa ya rasu.

Binciken farko ya nuna cewa mutuwar tasa ta samo asali ne daga karancin iskar oxygen da kuma tsananin zafin da ke cikin rijiyar.

Hukumar ta ce daga bisani an mika gawar marigayin ga shugaban unguwar Kwa, Alhaji Muktar, domin gudanar da shirye-shiryen jana’izarsa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments