Saturday, October 17, 2026
HomeTsaroGwamnatin Kano ta sha alwashin murkushe ayyukan daba a fadin Jihar

Gwamnatin Kano ta sha alwashin murkushe ayyukan daba a fadin Jihar

Gwamnatin Kano ta tsaurara matakai kan masu tada zaune tsaye.

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana kudirinta na kawo ƙarshen matsalar daba da sauran ayyukan ta’addancin matasa da ke haddasa tashin hankali a sassan jihar.

Babban Lauyan Jihar Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru Maude SAN, ne ya bayyana hakan a yayin wata hira da BBC, ya ce gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen hukunta duk wanda aka kama da hannu a ayyukan daba ko kuma wadanda ke tallafa musu ta kowace hanya.

Maude ya bayyana cewa karuwar rikice-rikicen daba a wasu yankunan jihar ta sa gwamnati ta dauki sabbin matakai domin dakile matsalar kafin ta kara kamari.

Ya ce ma’aikatar shari’a na aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro wajen bincike da tattara hujjoji kan mutanen da ake zargi da aikata laifuffuka, domin tabbatar da cewa an gudanar da shari’a bisa gaskiya da adalci.

Kwamishinan ya jaddada cewa duk lokacin da bincike ya tabbatar da akwai hujjoji kan wani mutum, gwamnati za ta tabbatar da an gurfanar da shi domin ya fuskanci hukuncin da doka ta tanada.

Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da hada kai da jami’an tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

SourceLegit
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments