Saturday, October 17, 2026
HomeTsaro’Yan bindiga sun hallaka mutum daya tare da sace masallata a Kaduna

’Yan bindiga sun hallaka mutum daya tare da sace masallata a Kaduna

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari wani masallaci da ke kauyen Unguwan Namama a yankin Kaya, karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna, inda suka kashe mutum daya tare da yin garkuwa da wasu masu ibada yayin da ake gudanar da sallar Magariba.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kutsa cikin kauyen da misalin karfe 7:30 na yammacin ranar Lahadi, kafin su nufi masallacin kai tsaye suka aiwatar da harin.

Wata majiya daga yankin ta bayyana cewa ana zargin harin na da nasaba da ramuwar gayya bayan wani samame da jami’an tsaro suka kai kwanakin baya, inda aka kashe wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne.

Majiyar ta ce maharan na kyautata zaton cewa wasu mazauna yankin ne suka bai wa jami’an tsaro bayanan sirri da suka taimaka wajen kai farmakin.

Hakan ne suka koma kauyen domin daukar fansa kan al’ummar yankin.

Har zuwa yanzu dai ba a tantance adadin mutanen da aka yi garkuwa da su ba, yayin da mazauna yankin ke cikin fargaba sakamakon harin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments