Majalisar Wakilai ta Najeriya ta sake jaddada muhimmancin kafa ’yan sandan jihohi a matsayin wani mataki na magance matsalolin rashin tsaro da ke ci gaba da addabar sassan kasar nan.
Haka kuma, majalisar ta bukaci Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro su gaggauta daukar matakan da suka dace domin kubutar da dalibai da malamai da aka yi garkuwa da su a jihohin Oyo da Borno.
An bayyana hakan ne yayin zaman majalisar bayan nazarin wasu kudurori biyu da suka shafi yawaitar sace-sacen mutane da hare-haren da ke barazana ga rayuka da dukiyoyin al’umma.
Dan majalisar da ke wakiltar mazabun Ogbomoso ta Arewa da ta Kudu a jihar Oyo, Olamijuwonlo Alao-Akala, ya nuna damuwa kan karuwar hare-haren masu garkuwa da mutane a yankunan Ogbomoso da Orire, yana mai cewa lamarin na yin barazana ga tsaro da kuma harkokin ilimi.