Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiNajeriya ce ta uku a duniya wajen cin bashin Bankin Duniya da...

Najeriya ce ta uku a duniya wajen cin bashin Bankin Duniya da dala biliyan 18.5

Najeriya ta ci gaba da riƙe matsayinta na uku cikin ƙasashen da suka fi karɓar bashi daga Bankin Duniya ta hannun IDA, inda bashinta ya kai dala biliyan 18.5 zuwa watan Maris 2026.

Najeriya ta ci gaba da riƙe matsayinta na uku cikin ƙasashen da suka fi karɓar bashi daga Bankin Duniya ta hannun IDA, inda bashinta ya kai dala biliyan 18.5 zuwa watan Maris 2026.

Ko da yake an samu ɗan ragi daga dala biliyan 18.7 a ƙarshen 2025, idan aka kwatanta da bara, bashin ya ƙaru da dala biliyan 1.2 daga dala biliyan 17.3.

Najeriya na biye bayan Bangladesh da Pakistan a jerin ƙasashen da suka fi cin bashin.

Gwamnatin tarayya na kuma neman sabon bashin dala biliyan 1.25 domin inganta wutar lantarki, ayyukan dijital, noma da kasuwanci.

Sai dai masana tattalin arziki sun yi gargaɗin cewa ci gaba da karuwar bashin na iya ƙara nauyi ga tattalin arzikin ƙasa, musamman ganin cewa jimillar bashin Najeriya ta kai Naira tiriliyan 159 zuwa shekarar 2025.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments