Sunday, October 18, 2026
HomeIlimiWAN, CELOHA sun yi Allah-wadai da cin zarafin dalibai mata hudu a...

WAN, CELOHA sun yi Allah-wadai da cin zarafin dalibai mata hudu a Kano

Kungiyoyin sun bukaci a yi gaggawar bincike da hukunta duk wanda aka samu da laifi a keta hakkin yara mata hudu a wata makaranta a Kano

Kungiyar West Africa Network for Child Protection (WAN) tare da hadin gwiwar Centre for Legal Orientation and Humanitarian Aid Initiative (CELOHA Nigeria), sun yi kakkausar suka kan zargin cin zarafi da fyade ga wasu kananan dalibai mata hudu da wani malami ya aikata a unguwar Dan Tamashe da ke Jihar Kano.

Kungiyoyin sun bayyana lamarin a matsayin babban take hakkin yara, wanda ya sabawa mutunci da kariyar da ya kamata yara su samu, tare da nuna damuwa kan tsaron dalibai a makarantu.

A cewarsu, makarantu ya kamata su kasance wuraren da yara ke samun ilimi, kariya da tarbiyya, ba wuraren da za su fuskanci cin zarafi, tashin hankali ko cutarwa ba.

WAN da CELOHA Nigeria sun kuma nuna damuwa kan yawaitar rahotannin cin zarafin yara a Najeriya, tare da abin da suka kira al’adar yin shiru da rashin hukunta masu aikata laifin, wanda ke kara ta’azzara matsalar.

Sun jaddada cewa duk wani nau’in cin zarafin yara abin Allah-wadai ne, kuma dole ne a dauki matakin doka cikin gaggawa ba tare da bata lokaci ba.

Kungiyoyin sun bukaci Gwamnatin Jihar Kano, Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya, Ma’aikatar Ilimi ta Kano, Ma’aikatar Harkokin Mata, da sauran hukumomin kare hakkin yara da su tabbatar da an gudanar da bincike na gaskiya, cikin adalci da kuma bayyana sakamakonsa.

Sun kuma bukaci cewa idan aka tabbatar da laifin wanda ake zargi, a gaggauta gurfanar da shi a gaban kotu, tare da kare mutuncin wadanda abin ya shafa.

Haka kuma sun nemi a samar wa yaran da abin ya shafa kulawar lafiya, tallafin tunani (psychosocial support) da shawarwari, tare da karfafa matakan kare yara a makarantu da inganta hanyoyin rahoton cin zarafi.

Kungiyoyin sun ce kare yara nauyi ne na kowa da kowa, wanda ya hada da gwamnati, makarantu, iyaye, shugabannin addini da na gargajiya, da kungiyoyin fararen hula.

WAN da CELOHA Nigeria sun sake jaddada kudirinsu na ci gaba da fafutukar kare hakkin yara, tabbatar da adalci da kuma kare wadanda aka ci zarafinsu, suna mai cewa babu yaro da ya kamata ya yi shiru cikin wahala.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments