Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaKotu ta tabbatar Jonathan na da damar tsayawa takarar shugaban ƙasa a...

Kotu ta tabbatar Jonathan na da damar tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027

Alkalin ya yi watsi da ƙarar da aka shigar kan tsohon shugaban ƙasar

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta bayyana cewa tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, na da damar tsayawa takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen shekarar 2027.

Mai shari’a Peter Lifu ne ya bayyana hakan yayin da yake yanke hukunci a wata ƙara da aka shigar domin hana Jonathan shiga kowace irin takarar shugaban ƙasa nan gaba, bisa hujjar cewa ya riga ya yi rantsuwar kama aiki sau biyu a matsayin shugaban ƙasa.

Sai dai alkalin ya yi watsi da ƙarar, yana mai cewa an kawo ta ne ta hanyar da ba ta dace ba kuma tana matsayin ɓata lokacin kotu.

A cewar Mai shari’a Lifu, Babbar Kotun Tarayya da kuma Kotun Ɗaukaka Ƙara sun riga sun yanke hukunci kan batun cancantar Jonathan, don haka babu wani sabon abu da zai ƙara.

Ya ce: “Ina bin hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara da wannan kotu suka riga suka yanke, babu wani ƙarin bayani da zan yi.”

Haka kuma kotun ta ci tarar mai ƙarar kuɗi har Naira miliyan 20 domin a bai wa Jonathan, sannan ta bayar da umarnin a biya Babban Lauyan Tarayya Naira miliyan 1.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments