Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiAmnesty International ta yi zargin Fulani 150 sun mutu a wani sansanin...

Amnesty International ta yi zargin Fulani 150 sun mutu a wani sansanin soja a jihar Kwara

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta zargi cewa akalla mutane 150 daga cikin al’ummar Fulani, ciki har da yara, sun mutu a wani wuri na tsare mutane da ke ƙarƙashin kulawar sojoji a Jihar Kwara.

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta zargi cewa akalla mutane 150 daga cikin al’ummar Fulani, ciki har da yara, sun mutu a wani wuri na tsare mutane da ke ƙarƙashin kulawar sojoji a Jihar Kwara.

Kungiyar ta kuma bukaci gwamnatin Najeriya da ta gudanar da bincike cikin gaggawa, mai zaman kansa kuma na gaskiya.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, Amnesty ta ce mutanen na daga cikin kusan Fulani makiyaya 1,500 da aka raba da muhallansu, waɗanda aka tsare a sansanin NYSC da ke Yikpata bayan sun tsere daga hare-haren tashin hankali a sassan jihar.

Kungiyar ta bayyana cewa mutanen da aka tsare sun fuskanci matsanancin cunkoso da rashin tsafta, ƙarancin abinci, kulawar lafiya, da kuma takaita musu ‘yancin motsi, wanda hakan ya janyo yunwa mai tsanani da cututtuka da suka bazu.

Daraktan Amnesty International a Najeriya, Isa Sanusi, ya ce Fulani na fuskantar tsanantawa ta bangarori biyu—daga kungiyoyin ‘yan bindiga da kuma daga jami’an tsaro. Ya kara da cewa maimakon a kare su, ana tauye musu hakkokinsu na ‘yanci, rayuwa, ilimi da kuma kiwon lafiya.

Binciken da kungiyar ta yi tsakanin 5 zuwa 11 ga Afrilu ya hada da tattaunawa da waɗanda suka tsira, iyalai da kuma wadanda abin ya shafa. Ta kuma ce hotunan da aka samu daga sansanin sun nuna yara da yunwa ta yi musu illa sosai har ana ganin ƙasusuwansu.

Wasu daga cikin wadanda suka tsira sun bayyana halin da suke ciki a matsayin mai matukar muni, suna cewa ana yawan mace-mace da kuma binne mutane da yawa a lokaci guda. Wata mata ta ce sun kan yi kwana ba tare da isasshen abinci ba, kuma yunwa ta kashe yara da mata masu juna biyu da dama, ciki har da ‘ya’yanta biyu.

Wani mutum mai shekaru 43 da ya yi tsere daga sansanin ya ce mutane 154 sun mutu tun bayan kawo su wurin, yana mai cewa a ranar da ya gudu ma yara shida sun mutu.

Amnesty ta ce tsare mutane bisa asalinsu na kabila wani nau’i ne na wariya da take hakkin bil’adama, tare da kira ga gwamnati da ta dakatar da irin wannan tsarewa ba bisa ka’ida ba, tare da tabbatar da adalci ga wadanda abin ya shafa.

Sai dai hedikwatar tsaro ta ƙasa ta musanta wannan zargi, tana cewa sansanin da ake magana a kai ba na sojoji ba ne. Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Manjo Janar Michael Onoja, ya ce sojoji ba su da alaka da wurin.

Hakazalika, gwamnatin Jihar Kwara ta nesanta kanta da lamarin, inda mai bai wa gwamna shawara kan harkokin yada labarai, Bashir Adigun, ya ce gwamnatin jihar ba ta da iko a kan irin wannan sansani.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a samu cikakken bayani daga rundunar soji ba dangane da zargin da Amnesty International ta yi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments