Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiYadda dalibin jami'ar Jos da aka sace ya samu ‘yanci

Yadda dalibin jami’ar Jos da aka sace ya samu ‘yanci

Dalibin Jami’ar Jos, John Arum Azi, wanda aka sace kusan makonni biyu da suka wuce, ya samu ‘yanci daga hannun masu garkuwa da shi. Ya kuma isa Jos, babban birnin Jihar Plateau, a daren Laraba da misalin karfe 10 na dare.

Dalibin Jami’ar Jos, John Arum Azi, wanda aka sace kusan makonni biyu da suka wuce, ya samu ‘yanci daga hannun masu garkuwa da shi.
Ya kuma isa Jos, babban birnin Jihar Plateau, a daren Laraba da misalin karfe 10 na dare.

An sace shi ne yayin tafiya, kuma wani bidiyo da aka yada a intanet yana nuna ana azabtar da shi ya jawo martani a fadin kasa da ma kasashen waje. Daga baya an kai shi daga Kaduna zuwa Zamfara, wanda ya jawo rade-radin cewa an kashe shi.

Sai dai a ranar Talata, wani gajeren bidiyo ya nuna cewa an sake shi kuma yana tare da wani da ake zaton dan uwansa ne.

Dan uwansa, Bulus, ya tabbatar cewa ya koma gida kuma an kwantar da shi a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos domin samun kulawa.

Ya ce Azi ya bayyana cewa ba a sace shi a hanyar Jos zuwa Kaduna ba kamar yadda aka ruwaito, sai dai a Zaria inda ya je neman aiki, kuma yana kan hanyarsa ta ganawa da wanda zai taimaka masa ne aka sace shi aka kai shi cikin daji.

Dangane da yadda aka sake shi, Bulus ya ce iyalansu sun rika tuntubar masu garkuwa da shi tun daga lokacin da aka sace shi, suna aika musu da kudi domin sayen kati da magunguna yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan kudin fansa.

Ya ce da farko sun amince kan Naira miliyan 6, amma bayan ganin yadda aka fara tara kudi a intanet, masu garkuwar suka kara kudin zuwa miliyan 15. Daga baya, bayan roko, aka daidaita kan Naira 10,315,000 wanda aka biya.

Bayan an biya kudin, an kawo shi da wani da aka sace tare da shi daga Zamfara zuwa Zaria a kan babura, tare da wani mai dauke da makami yana binsu a baya.

Da suka isa Zaria, dayan mutumin ya tuntubi danginsa, wanda ya kai su asibiti aka fara kula da su. Daga baya iyalan Azi suka dauki mota daga Jos zuwa Zaria domin dauko shi.

Ya ce Azi ya iso Jos da daddare kuma aka garzaya da shi JUTH, yana da raunuka da tabo a jikinsa sakamakon dukan da aka yi masa.

Game da hukumomin tsaro, ya ce sun kai rahoto ga ‘yan sanda da DSS tun farko, amma bayan an sake shi ne ‘yan sanda suka sake tuntubar su bayan sun ga bidiyo a intanet, inda suka ba da taimakon rakiyar su, amma sun iso ne bayan an riga an dauke shi zuwa asibiti.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments