Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiEl-Rufai ya gurfana a kotu kan zargin satar bayanan wayar Nuhu Ribadu

El-Rufai ya gurfana a kotu kan zargin satar bayanan wayar Nuhu Ribadu

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya gurfana a gaban kotu bisa zargin satar bayanan wayar Nuhu Ribadu.

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya gurfana a gaban kotu bisa zargin satar bayanan wayar Nuhu Ribadu.

Ana tuhumarsa da samun damar bayanan sirri ba tare da izini ba, musamman dangane da tattaunawar wayar da ta shafi tsaron ƙasa.

Hukumar tsaro ta DSS ta shigar da ƙara a kansa kan zargin keta dokokin tsaro da kuma aikata laifukan yanar gizo, ciki har da sa ido ko sauraron wayoyin manyan jami’an gwamnati ba tare da izinin doka ba.

A cewar masu gabatar da ƙara, wannan mataki na iya zama barazana ga tsaron ƙasa da lafiyar jama’a. Sai dai El-Rufai ya musanta laifin, yana mai cewa zai kare kansa a kotu.

Kotun ta dage sauraron ƙarar domin ci gaba da shari’a yayin da ake sa ran bincike da shaidu za su fito da gaskiyar lamarin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments