Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiKwastam ta kama wasu dabbobi da aka yi ƙoƙarin shigar da su...

Kwastam ta kama wasu dabbobi da aka yi ƙoƙarin shigar da su Najeriya ba bisa ka’ida ba

Hukumar hana fasa-ƙwauri ta Najeriya ta ƙwace miyagun ƙwayoyi da namun daji da ke fuskantar barazanar ƙarewa a Maiduguri da ke Arewa maso gabashin Najeriya.

Wata sanarwa da hukumar ta kwastam ta wallafa a shafinta na X ranar juma’a ta ce jami’anta sun ƙwace buhuna 180 na miyagun ƙwayoyin da ake kira a-kurkura da kuma wasu namun dajin da ke fuskantar barazanar ƙarewa a wasu samame da suka kai kan hanyar Kano zuwa Maiduguri a jihar Borno.

Shugaban hukumar kwastam a yankin, Comptroller Idris Abdullahi ne ya sanar da haka yayin da yake zanta wa da manema labarai a hedkwatar rundunar ta yankin da ke Maiduguri.

Ya bayyana cewa an yi kamen na farko ne ranar Laraba, 15 ga watan Afrilu na shekarar 2026, bayan an samu bayanan sirri inda jami’ai suka kama wata mota ɗauke da buhuna 180 na miyagun ƙwayoyi da ake ce wa Akuskura.

A wani samamen na daban kuma ranar Litinin, 20 ga watan Afrilun shekarar 2026, rundunar ta yi nasarar ƙwace wasu namun dajin da ake safararsu a kan hanyar.

Dabbobin sun haɗa da bareyi biyu da matacciyar barewa da beguwa ɗaya da magen juda biyu da mikiya huɗu da kuma kunkuru 13 masu rai.

Sanarwar ta ce bincike na farko-farko ya nuna cewa dabbobin suna cikin jerin namun dajin da dokokin ƙasa da ƙasa da Najeriya ta sanya wa hannu suka hana safararsu.

SourceTRT
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments