Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya soki Peter Obi kan zargin yin munafunci sakamakon kalaman yabo da ya ke yi wa yankin Arewacin Najeriya.
Peter Obi, wanda ya kasance jigon jam’iyyar ADC ya bayyana cewa zai ba wa cigaban Arewacin Najeriya fifiko, inda ya siffanta yankin a matsayin babbar kadara ga ƙasar nan.
Da yake mayar da martani, Sowore ya tunatar da ‘yan Arewacin Najeriya wani tarihi da ya shuɗe.
Ya bayyana cewa a lokacin da Peter Obi yake matsayin Gwamnan Jihar Anambra, ya taɓa ba da umarnin a kamo ‘yan Arewa mazauna jihar sannan aka tisa keyarsu aka mayar da su yankunansu na asali.
A cewar Sowore, hakan na nuna cewa yabon da Obi ke yi wa Arewa a yanzu na neman ƙuri’a ne kawai ba don yana ƙaunarsu ba.