A yau aka gurfanar da sojoji 36 da ake zargi da yunkurin juyin mulki ga Shugaban Najeriya Bola Tinubu, gaban Kotun Soji na musamman a Abuja, bayan da Hedikwatar Tsaro ta kafa kwamitin masu shari’a.
Hedikwatar Tsaro ba ta yi wani sanarwa kan matakin ba, sai dai rahotanni na cewa kotun za ta yi zamanta a ɗakin taron manyan hafsohi na Scorpion da ke Asokoro a babban birnin tarayya Abuja a ranar 23 ga wataan Afrilu, bisa ga umarnin da AM Alechenu, Kwamandan sashin Garrison na Hedikwatar Tsaro ya sanya wa hannu.
Umarnin, wanda aka sanya wa hannu a ranar 17 ga watan Afrilu, ya bayyana cewa haɗakar ‘yan sandan soji da ‘yan sandan ruwa da na sama, gami da jami’an tsaron fadar shugaban ƙasa za su yi gadin kotun.
Umarnin ya ce, ba amince kowa ya shigo da makamai cikin ɗakin shari’ar ba, sai masu gadin kotu waɗanda aka ba su izinin.
A cewar umarnin, an kafa tawagar masu shari’ar ne bisa ga Dokar Sojojin ta Cap A20 ta Dokokin Tarayyar Najeriya ta shekarar 2004.
Tawagar alkalan ta ƙunshi manyan hafsoshi daga Sojojin Ruwa da Sama da kuma na ƙasa ƙarƙashin wani babban jami’i.
Waɗanda za a gurfanar na daga cikin wani rukunin jami’an tsaro da aka tsare tun shekarar 2025, sakamakon zarginsu da yunkurin juyin mulki da bai yi nasara ba.
Lamarin ya fara fita ne tamkar jita-jita, cewa an kama wasu jami’ai kan zargin juyin mulki, sai dai hukumomi harda rundunar sojin Najeriya sun yi watsi da ikirarin, kafin daga bisani suka amince cewa shirin kifar da gwamnatin Mista Tinubu gaskiya ne.