Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeIran ta wallafa bidiyon yadda dakarunta suka kwace jiragen ruwa a Hormuz

Iran ta wallafa bidiyon yadda dakarunta suka kwace jiragen ruwa a Hormuz

Rahotanni sun ce bidiyon ya nuna yadda aka kwace jiragen ruwa guda biyu tare da kai su zuwa gabar Iran.

Iran da Amurka na ci gaba da musayar kalamai masu zafi a Gabas ta Tsakiya, duk da tsagaita wutar da Donald Trump ya sanar.

Iran ta cigaba da farautar jiragen ruwan da suke yunkurin wucewa ta mashigar Hormuz bayan rufe shi da ta yi a karshen makon da ya wuce.

Rundunar juyin juya halin Iran ta fitar da wani bidiyo da ya nuna yadda sojojinta suka kama wani jirgin ruwa a mashigar Hormuz.

Rahotanni sun nuna cewa jirgin ɗaukar kayan na daga cikin jirage biyu da Iran ta kama a ranar Laraba, 22 ga watan Afrilun 2026.

Iran ta ce jiragen suna aiki ba tare da izinin dakarun sojinta ba, kuma sun yin katsalandan ga tsarin tafiya na jiragen ruwa a Hormuz.

A bidiyon da Al Jazeera ta wallafa a X, an hango sojojin Iran na fitowa a cikin jirginsu suna karkatar da jirgin ruwan

SourceLegit
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments