Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeWasu jami’an Najeriya na da hannu a kashe-kashen Kiristoci – Sanatan Amurka

Wasu jami’an Najeriya na da hannu a kashe-kashen Kiristoci – Sanatan Amurka

Sanata daga Amurka, Ted Cruz, ya zargi wasu jami’an gwamnati a Najeriya da hannu wajen taimakawa ko sauƙaƙa kisan Kiristoci a ƙasar.

Sanata daga Amurka, Ted Cruz, ya zargi wasu jami’an gwamnati a Najeriya da hannu wajen taimakawa ko sauƙaƙa kisan Kiristoci a ƙasar.

Ya bayyana hakan ne yayin wani taron kwamitin harkokin waje na majalisar dattawan Amurka, inda aka tattauna kan dabarun yaki da ta’addanci a nahiyar Afirka.

A cewarsa, Najeriya na daga cikin ƙasashen da ake kashe Kiristoci mafi yawa a duniya saboda addininsu. Ya ƙara da cewa tun daga shekarar 2009, sama da mutane 50,000 Kiristoci aka kashe, yayin da fiye da cibiyoyi 20,000 da suka haɗa da majami’u da makarantu aka lalata.

Cruz ya ce abin takaici ne yadda, a cewarsa, wasu jami’an Najeriya ke da hannu ko kuma suna ba da damar faruwar irin waɗannan hare-hare.

Sai dai kuma, a gefe guda, wasu jami’an gwamnatin Najeriya sun sha musanta zargin cewa ana kai hari ne kai tsaye ga wani addini guda, suna cewa matsalar tsaro a ƙasar tana shafar kowa, Musulmi da Kiristoci, ba tare da bambanci ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments