Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGwamnati ta musanta zargin da kungiyoyin farar hula na Najeriya na dab...

Gwamnati ta musanta zargin da kungiyoyin farar hula na Najeriya na dab da rugujewa

Gwamnatin tarayyar kasar nan ta musanta zargin da kungiyoyin farar hula ke yi cewa kasar na dab da rugujewa, tana mai cewa a maimakon haka, kasar nan na nuna juriyar ci gaba da farfadowa a fannoni daban-daban.

Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, ya bayyana haka a taron BON a Abuja, inda ya ce irin wadannan hasashe ba su da tushe, yana mai jaddada cewa ana magance matsalolin tsaro da tattalin arziki cikin tsari.

Ya bayyana cewa an samu nasarori a bangaren tsaro sakamakon hadin gwiwar rundunoni da ingantaccen musayar bayanan sirri, wanda ya taimaka wajen dakile hare-hare da kuma rage karfin ‘yan bindiga musamman a Zamfara da Neja.

Haka kuma, ya ce an rage ikon da ‘yan ta’adda ke da shi a wasu yankuna, tare da kara inganta tsarin daukar matakin gaggawa domin kare rayuka da dukiyoyi.

A bangaren tattalin arziki, ministan ya nuna cewa akwai alamun farfadowa da karin amincewar masu zuba jari, sakamakon sauye-sauyen da gwamnati ke aiwatarwa domin inganta gaskiya da daidaita harkokin kudi.

Ya kara da cewa ajiyar kudaden waje na karuwa, sannan hanyoyin samun kudaden shiga na fadada a bangaren man fetur da wadanda ba na man fetur ba.

Mohammed Idris ya kuma ambaci yadda aka sake bai wa Najeriya matsayi na “Frontier Market” daga FTSE Russell, yana mai cewa hakan na nuna ingantuwar kasuwar kudi, samun kudin musayar waje, da saukin jawo jarin kasashen waje. Ya ce wannan na kara tabbatar da cewa Najeriya na dawowa a matsayin wuri mai kyau ga masu zuba jari na duniya.

Dangane da kafafen yada labarai, ya bukaci a rika aikin jarida cikin gaskiya da rikon amana, musamman yayin da zabuka ke karatowa, Ya jaddada cewa wajibi ne masu watsa labarai su guji yada labaran da ke haddasa rarrabuwar kawuna ko tsoro, su kuma taimaka wajen hada kan al’umma.

Ministan ya sake tabbatar da goyon bayan gwamnati ga ‘yancin ‘yan jarida, tare da kira ga hadin gwiwa tsakanin gwamnati da kafafen yada labarai domin yakar bayanan karya da inganta hadin kan kasa.

Ya kuma yabawa BON da sauran masu ruwa da tsaki kan kokarinsu na inganta kwarewa da da’a a harkar yada labarai.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments