Wasu ‘yan bindiga sun kashe akalla mutane biyar tare da yin garkuwa da wasu 22 a hare-hare daban-daban da suka kai da tsakar dare a al’ummomi uku na karamar hukumar Sabon Birni a Jihar Sokoto.
Majiyoyi sun ce hare-haren sun faru ne tsakanin karfe 11 na dare zuwa 12 na dare a garin Sabon Birni, Dan Aduwa da Kwaren Gamba.
A garin Sabon Birni, an ce maharan sun shigo ta unguwar Sabon Hegi daga gefen makabarta, inda suka rika harbe-harbe ba kakkautawa, abin da ya jefa jama’a cikin firgici. Wasu mazauna yankin sun ce mutane sun rika gudu suna neman mafaka.
Mutane biyu da aka gano su ne Abbas Sani da Bala Mai Laya Moriki waɗanda suka rasa rayukansu, yayin da aka sace wasu takwas. Daga cikin wadanda aka sace har da wani makaho, wanda aka ce an dauke shi ba tare da ya san abin da ke faruwa ba.
Haka kuma, wasu daga cikin wadanda aka kashe da kuma wadanda aka sace sun zo ne daga Moriki a Jihar Zamfara domin kasuwancin kifi.
A halin yanzu, mutane biyar da suka jikkata na karbar magani a Asibitin Gwamnati da ke Sabon Birni. Mazauna yankin sun ce jami’an tsaro sun isa wurin kusan mintuna 20 bayan maharan sun tsere.
A kauyen Dan Aduwa kuwa, ‘yan bindiga sun kai hari da tsakar dare, inda suka sace mutane uku ciki har da ‘yan mata masu raka amarya biyu da wani namiji.
Wani mazaunin yankin ya danganta harin da harbe-harben biki da matasa suka yi kafin faruwar lamarin.
Wadanda aka sace sun hada da Sabiu Saidu, Balira Halliru da Maryam Mansur, kuma ba a samu asarar rai ko rauni ba a wannan kauyen.
A Kwaren Gamba kuwa, maharan sun iso ne a kan babura da misalin karfe 11:05 na dare, inda suka kashe mutane uku tare da sace wasu 11, ciki har da maza shida da mata biyar. Wadanda aka kashe sun hada da Malam Yakubu, dansa Kabir Yakubu da wani mutum mai suna Yakubu.
Majiyoyi sun ce daga baya jami’an tsaro sun isa wurin, lamarin da ya hana kara asarar rayuka.
Dan majalisar dokokin jihar da ke wakiltar Sabon Birni ta Arewa, Aminu Boza, ya tabbatar da faruwar hare-haren, amma bai bayyana adadin wadanda suka mutu ba.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Ahmad Rufai, ya ce har yanzu bai samu cikakken bayani daga jami’an yankin ba.