Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiTinubu ya ware Naira tiriliyan 3.3 domin magance bashin lantarki

Tinubu ya ware Naira tiriliyan 3.3 domin magance bashin lantarki

Shugaba Tinubu ya ba da umarni kan fitar da Naira tiriliyan 3.3 don warware bashin wuta.

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da wani shirin biyan kuɗi har Naira tiriliyan 3.3 domin warware tsofaffin basussukan da suka addabi ɓangaren wutar lantarki, a wani mataki da ake ganin zai taimaka wajen farfaɗo da tsarin samar da wuta da kuma inganta ayyukansa gaba ɗaya.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa wannan mataki ya biyo bayan cikakken nazari kan basussukan da suka taru tsawon sama da shekaru goma, daga watan Fabrairu na 2015 zuwa Maris 2025, inda aka tabbatar da cewa adadin Naira tiriliyan 3.3 shi ne cikakken kuɗin da za a biya domin rufe wannan lamari gaba ɗaya.

Ya ƙara da cewa tuni aka fara aiwatar da shirin, inda tashoshin samar da wutar lantarki guda 15 suka rattaba hannu kan yarjejeniyar karɓar bashin da ya kai Naira tiriliyan 2.3, yayin da gwamnatin tarayya ta tara Naira biliyan 501 domin fara biyan kuɗin, ciki har da Naira biliyan 223 da aka riga aka fitar, tare da ci gaba da sauran biyan kuɗaɗen a matakai na gaba.

SourceDCL
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments