Yusuf, ɗan marigayi tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar Majalisar Wakilai.
Tun da farko an ruwaito cewa wasu jiga-jigan APC sun goyi bayansa domin tsayawa takarar kujerar Daura, Sandamu da Mai’Adua.
Sai dai wasu ‘yan jam’iyyar APC daga kananan hukumomi biyar na Masarautar Daura sun yi alkawarin kin amincewa da duk wani yunkuri na kakaba musu dan takara, suna masu cewa za su ci gaba da bin tsarin dimokuradiyya na jam’iyya.
A wata wasika da aka ce Yusuf ya rubuta ranar 3 ga Afrilu, ya sanar da masu ruwa da tsaki cewa ya yanke shawarar tsayawa takarar kujerar.
Ya ce: “Ina farin cikin sanar da ku aniyata ta tsayawa wannan takara domin ba da gudunmawa ga shugabanci nagari da kuma kawo ci gaba ga al’ummarmu.”
Wani jigo ya tabbatar da hakan, yana mai cewa Yusuf ya dauki wannan mataki ne bayan tuntubar masu ruwa da tsaki da dama.