Tsohon ɗan takarar shugabancin Najeriya, Peter Obi, ya nuna matuƙar damuwa kan yawaitar hare-hare da ajalin mutane a faɗin Najeriya, yana mai tambayar sahihancin alkawarin da shugaba Tinubu ya yi dangane da tsaro.
Rahotanni sun bayyana cewa Obi na bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, bayan ziyarar da Tinubu ya kai jihar Filato a ranar 2 ga Afrilu, 2026, inda ya yi alƙawarin cewa irin hare-haren da suka faru ba za a sake maimaitasu ba.
Obi ya ce cikin ƙasa da awanni 24 bayan wannan alƙawari, an sake kai wani hari a Nyamgo Gyel da ke Jos ta Kudu, inda aka halaka mutane da dama, kuma ya ambaci sabbin hare-hare a jihohin Nasarawa, Zamfara da Borno, ciki har da sace mutane da dama da kuma halaka jami’an tsaro a Chibok.