Gwamnan jihar Borno ya dauki matakin sauke dukkan kwamishinoni domin sake gina tsarin shugabanci.
A cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jiha, Bukar Tijani, ya fitar, ta ce an dauki matakin ne domin samar da damar da zata bai wa duk wani dan majalisar da ke son tsayawa takara a zabukan gaba damar yin hakan.
Gwamnan ya umarci dukkan kwamishinoni da su mika ragamar ma’aikatunsu ga manyan sakatarorin ma’aikatun da suke kafin ranar Juma’a, 3 ga Afrilu, 2026.
Gwamna Zulum ya kuma gode wa kwamishinonin da suka bisa gudunmawar da suka bayar, jajircewa da sadaukarwa wajen hidimtawa al’ummar Jihar ta Borno.