Tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Kano a zaɓen 2023, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, ya dankwafar da shahadar sa ta zama ɗan jam’iyyar APC.
A cikin wasiƙar murabus da ya rubuta ranar 29 ga Maris ɗin 2026, ya bayyana cewa matakin nasa na barin jam’iyyar na radin kai ne. Ya ce, “Ina sanar da ku a hukumance cewa na ajiye shahadata ta zama ɗan jam’iyyar APC daga ranar 29 ga Maris na shekarar 2026.”
Ya kuma gode wa jam’iyyar bisa damar da ta ba shi yayin da yake cikinta. Sai dai bai bayyana matakin siyasa na gaba da zai ɗauka ba.
Sai dai ana ganin wannan mataki a matsayin wani ɓangare na sauye-sauyen siyasa da ke faruwa a jihar, musamman bayan yawaitar sauya sheƙa tsakanin ‘yan siyasa.
A halin yanzu, wasu majiyoyi sun ce ana sa ran Gawuna zai gana da tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya koma jam’iyyar ADC, domin tattaunawa a gidansa da ke Miller Road.