Shugaba Bola Tinubu ya sanar da bayar da dukkan albashinsa ga sojojin da suka jikkata a bakin aiki da kuma iyalan wadanda suka rasu.
Haka kuma, ya kafa wani asusun tallafi na musamman domin kula da irin wadannan mutane.
Shugaban ya bayyana wannan shiri ne a ranar Lahadi yayin bikin cika shekaru 74 da haihuwarsa, domin girmama jarumtaka, sadaukarwa da hidimar sojojin kasar nan.
Ya umarci Akanta Janar na Tarayya da ya bude wani asusu na musamman domin wannan shirin, wanda zai tallafa wa sojojin da suka jikkata da kuma zawarawa, mazajen da suka rasa matansu, da ‘ya’yan wadanda suka rasu suna yi wa kasa hidima.