Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiA karon farko dan Najeriya ya zama mukaddashin Sakatare Janar na CAF.

A karon farko dan Najeriya ya zama mukaddashin Sakatare Janar na CAF.

An naɗa ɗan Najeriya, Samson Adamu, a matsayin mukaddashin Sakatare Janar na Hukumar kwallon Kafa ta Afirka wato CAF.

An naɗa ɗan Najeriya, Samson Adamu, a matsayin mukaddashin Sakatare Janar na Hukumar kwallon Kafa ta Afirka wato CAF.

Rahoton hukumar dillancin labarai na kasa NAN, ya bayyana cewa Adamu shi ne ɗan Najeriya na farko da ya riƙe wannan muƙami tun bayan kafuwar CAF sama da shekaru 70 da suka wuce.

A wata sanarwa da Daraktan Sadarwa na Hukumar kwallon Kafa ta Najeriya NFF, Ademola Olajire, ya fitar, ya ce Adamu ya maye gurbin Veron Mosengo-Omba na Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo, wanda ya sauka daga muƙamin domin tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙungiyar ƙwallon ƙafarsu wato FECOFA.

Kafin wannan naɗi, Adamu ya kasance Daraktan Gasar Kwallo da Shirye-shirye na CAF, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen shirya manyan gasannin nahiyar Afirka.

An gabatar da sunansa ne daga Kwamitin Zartarwa na CAF, sannan taron ƙungiyar ya amince da shi a zamansu da aka yi ranar 29 ga Maris, 2026 a birnin Cairo.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments