Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiAn kama waɗanda ake zargi da satar mutane a jihar Plateau.

An kama waɗanda ake zargi da satar mutane a jihar Plateau.

Jami'an rundunar ƴan sandan jihar Plateau sun kama sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da satar mutane da kuma fashi da makami ga wani mai neman shiga aikin ‘yan sanda.

Jami’an rundunar ƴan sandan jihar Plateau sun kama sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da satar mutane da kuma fashi da makami ga wani mai neman shiga aikin ‘yan sanda.

Lamarin ya faru ne a ranar 26 ga Fabrairun 2026, da misalin ƙarfe 3:00 na rana, lokacin da aka tare mutumin yayin da yake dawowa ƙaramar hukumar Qua’anpan bayan kammala tantancewa.

‘Yan bindigar sun ƙwace masa wayarsa ta Samsung Galaxy A8, power bank da kuma kuɗi Naira 25,000, sannan suka tafi da shi zuwa wani daji a Gada Biu inda suka tsare shi na wani lokaci kafin daga bisani su sake shi.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Bassy Ewan, ya bayyana sunayen waɗanda aka kama da Prince Bernard Bassey mai shekaru 25 daga jihar Cross River da kuma Sunday Laraba daga ƙaramar hukumar Bassa a Plateau.

Ya ce bayan samun rahoto, an umarci sashen yaƙi da satar mutane da su ɗauki mataki nan take, inda aka kama waɗanda ake zargin a Gada Biu da ke Jos.

An kuma kwato wasu kayayyaki daga hannunsu ciki har da miyagun ƙwayoyi, makamai masu haɗari da katunan SIM da dama.

A yanzu haka suna hannun ‘yan sanda yayin da ake ci gaba da bincike, kuma za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments