Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiAPC na cikin fargaba duk da rinjayen gwamnoni da ƴan majalisa –...

APC na cikin fargaba duk da rinjayen gwamnoni da ƴan majalisa – ADC

Jam’iyyar ADC ta soki jam’iyyar APC, tana mai cewa har yanzu tana cikin fargaba duk da rinjayen da take da shi kafin zaɓen 2027.

Jam’iyyar ADC ta soki jam’iyyar APC, tana mai cewa har yanzu tana cikin fargaba duk da rinjayen da take da shi kafin zaɓen 2027.

ADC ta bayyana cewa duk da APC na da gwamnoni 31 da kuma kusan kashi 90 cikin 100 na ‘yan majalisar tarayya, har yanzu tana nuna alamun tsoro.

Sakataren yaɗa labarai na ƙasa na ADC, Bolaji Abdullahi, ne ya bayyana hakan a wata hira a Channels TV, inda ya tambayi dalilin da yasa jam’iyya mai irin wannan ƙarfi ke nuna damuwa.

Ya ce a zahiri irin wannan rinjaye ya kamata ya ba su kwarin gwiwa, amma akasin haka ake gani.

Ya kuma zargi APC da ƙoƙarin dagula jam’iyyun adawa saboda tsoron sakamakon zaɓe na gaskiya da adalci.

A cewarsa, idan aka yi zaɓe na gaskiya a Najeriya, APC ba za ta iya yin nasara ba, domin ‘yan Najeriya sun gaji da mulkinta.

Har ila yau, ya ce APC ta yi matuƙar dogaro ga Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa idan mulkinsa ya ƙare, jam’iyyar na iya fuskantar matsala wajen ci gaba da haɗin kai.

Ya ƙara da cewa ADC na kokarin amfani da tsarin sasanci wajen zaɓen ɗan takararta na shugaban ƙasa a 2027, domin rage kashe kuɗi da kuma ƙarfafa haɗin kai a cikin jam’iyyar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments