Saturday, October 17, 2026
HomePress ReleaseYan kasuwa sun roƙi a inganta kasuwar tumatir da rumfuna, ruwa da...

Yan kasuwa sun roƙi a inganta kasuwar tumatir da rumfuna, ruwa da masallaci

Yan kasuwa sun jaddada bukatar samar da rumfuna, ruwan sha da masallaci a sabuwar kasuwa.

Yan kasuwar Tumatir sun yi kira ga Shugaban Karamar Hukumar Bagwai da ya gaggauta samar da muhimman kayayyakin more rayuwa a sabuwar Kasuwar Tumatir ta Marafa, domin inganta harkokin kasuwanci da walwalar ‘yan kasuwa a yankin.

Kiran ya fito ne yayin wata ganawa da Jami’in Yaɗa Labarai na Yankin Malam Shehu Bello Shanono da ya hada da ‘yan kasuwa, dillalai da masu ruwa da tsaki, inda suka bayyana bukatar gina tsararrun rumfuna, samar da ingantaccen ruwan sha, da kuma gina masallaci domin saukaka gudanar da ibada da kasuwanci cikin tsari.

A yayin tattaunawar sun jaddada cewa rashin wadannan muhimman abubuwa na Iya kawo cikas ga ci gaban kasuwar, tare da rage ingancin mu’amala da kuma jin dadin masu saye da sayarwa.

Sun kara da cewa samar da wadannan kayayyaki zai taimaka wajen kara habaka tattalin arzikin yankin.

Da yake nasa jawabin, Shugaban Dillalan Masu Sayan Tumatir, Alhassan Usman, ya bayyana cewa wannan bukata ta zama wajibi, inda ya roki Shugaban Karamar Hukumar da ya dauki matakin gaggawa.

Ya kara da cewa samar da rumfuna da ruwan sha zai taimaka wajen kare lafiyar ‘yan kasuwa da kuma tabbatar da dorewar kasuwanci.

Shi ma da yake jawabi, Shugaban Kungiyar ‘Yan Kasuwar, Ya’u Shafiu Kwajale, ya bayyana cewa gina masallaci a cikin kasuwar zai ba ‘yan kasuwa damar gudanar da ibadarsu cikin sauki ba tare da tangarda ga harkokinsu ba.

Daga nan, ya kuma yabawa kokarin gwamnati a wasu bangarori, tare da fatan za a dauki wannan bukata da muhimmanci.

Hakazalika sun bukaci Shugaban Karamar Hukumar Bagwai da ya duba wannan kira cikin gaggawa, domin tabbatar da cewa sabuwar Kasuwar Tumatir ta Marafa ta zama abin koyi a fannin tsari, tsafta da ci gaban kasuwanci.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments