Saturday, October 17, 2026
HomePress ReleaseRundunar ’Yan Sandan Kano ta ayyana dokar hana zirga-zirga yayin zaben cike...

Rundunar ’Yan Sandan Kano ta ayyana dokar hana zirga-zirga yayin zaben cike gurbi

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta sanar da sanya dokar hana zirga-zirga a ƙananan hukumomin Dawakin Kudu da Warawa gabanin zaɓen cike gurbin ɗan Majalisar Wakilai da za a gudanar ranar Asabar.

Sanarwar ta ce dokar za ta fara aiki daga ƙarfe 12:00 na rana zuwa ƙarfe 5:00 na yamma ranar 20 ga Yuni, 2026, domin tabbatar da tsaro, zaman lafiya da kuma gudanar da sahihin zaɓe.

An bayyana cewa dokar ba ta shafi jami’an tsaro, ma’aikatan INEC, masu sa ido kan zaɓe da aka tantance, da kuma ’yan jarida masu ingantacciyar shaidar aiki.

Rundunar ta kuma ce an tura jami’an tsaro zuwa rumfunan zaɓe, cibiyoyin tattara sakamako, ofisoshin INEC da sauran wurare masu muhimmanci domin kare lafiya da dukiyoyin al’umma.

Kazalika, Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya gargadi jam’iyyun siyasa da magoya bayansu da su guji duk wani abin da zai iya kawo cikas ga zaman lafiya, tare da hana kamfe ko nuna alamun jam’iyya cikin tazarar mita 300 daga rumfunan zaɓe.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments