Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana dalilin da ya sa aka kafa APC.
A yayin babban taron jam’iyya na ƙasa da ake gudanarwa a Abuja, Tinubu ya bayyana cewa an kafa APC ne domin kawo sauyi a ƙasa, rage talauci, inganta tsaro da kuma farfaɗo da manyan cibiyoyin gwamnati.
Tinubu, wanda ya bayyana haka a ranar Juma’a ya jaddada cewa ba wai an kafa APC don cin zaɓe ba kawai, sai dai a matsayin wata kafa da ke da burin gina Najeriya.
Ya ƙara da cewa jam’iyyar ta kasance “gida ga duk wanda ke son ganin an gina ƙasa inda gwamnati ke aiki yadda ya kamata, tabbatar da tsaro da magance talauci kuma kowanne ɗan Najeriya ya rayu cikin mutunci da fata.”
Shugaban ya kuma tuna cewa an kafa APC shekaru 13 da suka gabata ne sakamakon haɗin gwiwar ƴan siyasa da suka haɗa kai domin ceto ƙasar daga matsalolin tattalin arziki a wancan lokaci, yana mai cewa har yanzu jam’iyyar na tsaye kan manufofin dimokuraɗiyya da ke tabbatar da adalci, ci gaba da walwalar al’umma baki ɗaya.