Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiLabaraiINEC ta kara wa'adin rajistar jam'iyyu gabanin zaɓen 2027

INEC ta kara wa’adin rajistar jam’iyyu gabanin zaɓen 2027

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta ƙara wa’adin ƙarshe na miƙa rajistar mambobin jam’iyyun siyasa zuwa ranar 10 ga Mayu, 2026, gabanin zaɓen 2027.

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta ƙara wa’adin ƙarshe na miƙa rajistar mambobin jam’iyyun siyasa zuwa ranar 10 ga Mayu, 2026, gabanin zaɓen 2027.

Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Kwamishinanta na ƙasa kuma shugaban kwamitin yaɗa bayanai da ilimantar da masu zaɓe, Mohammed Kudu Haruna, ya fitar, inda ya ce an ɗauki wannan mataki ne bayan tattaunawa da jam’iyyun siyasa.

A cewarsa, sabon wa’adin ya maye gurbin ranar 21 ga Afrilu, 2026 da aka fara sanya a jadawalin da aka sabunta.

Ya bayyana cewa jam’iyyun siyasa sun nuna damuwa kan gajeren lokacin da aka ba su wajen miƙa rajistar mambobinsu, wanda hakan ya sa hukumar ta sake duba wa’adin domin ya dace da dokar zaɓe.

Har ila yau, ya ƙara da cewa dole ne jam’iyyun su miƙa rajistar mambobinsu ga INEC aƙalla kwanaki 21 kafin gudanar da zaɓen fidda gwani, kamar yadda doka ta tanada.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments