Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaKwankwaso ya gana da jiga-jigan jam’iyyar ADC

Kwankwaso ya gana da jiga-jigan jam’iyyar ADC

Ana ci gaba da hasashen sauya shekar Kwankwaso, inda ya gana da wasu jiga-jigan ADC an Abuja.

daidai lokacin da jita-jitar sauya shekar Sanata Rabiu Kwankwaso ke ƙaruwa, jagoran NNPP ya gana da shugabannin ADC a Abuja.

Yayin da zaben 2027 ke kara karatowa, Rabiu Musa Kwankwaso ya gana da Rauf Aregbesola da shugabannin ADC a Abuja Hakan na zuwa ne yayin da ake rade-radin cewa Sanata Rabiu Kwankwaso zai fita daga NNPP zuwa jam’iyyar hadakar ‘yan adawa ta ADC.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya sanar da ganawar shi da sakararen jam’iyyar ADC, Rauf Aregbesola.

Bayan ganawarsu, Kwankwaso ya ce: “Na ji daɗin karɓar baƙuncin tsohon gwamnan jihar Osun kuma sakataren jam’iyyar ADC na kasa, Rauf Aregbesola, a gidana da ke Abuja.”

Duk da Kwankwaso bai yi karin bayani game da abubuwan da suka tattauna ba, sai dai ana hasashen ganawarsu na da nasaba da shirin shigarsa ADC.

SourceLegit
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments