Domin kyautata kula da marasa lafiya, gwamnatin Kano ta bullo da shirin ziyarar bazata a asibitocin jihar.
Jami’ar hulɗa da jama’a ta Hukumar kula da asibitoci ta jihar Samira Suleiman ce ta fitar da sanarwar.
Sanarwar ta bayyana cewa Shugaban Hukumar, Dakta Mansur Mudi Nagoda ya ce an ɗauki matakin ne domin gyara kura-kurai da kuma tabbatar da bin ƙa’idojin aiki yadda ya kamata.
Ya umarci shugabannin asibitoci da su tabbatar da tsara jadawalin aiki dan amfani da shi sau da ƙafa, tare da kula da tsafta a kowane lokaci.
Hukumar ta ce ba za ta lamunci rashin zuwa aiki ba, tare da jaddada muhimmancin mika aiki yadda ya kamata tsakanin ma’aikata domin kauce wa tangarda wajen kula da marasa lafiya.
Haka kuma hukumar ta buƙaci marasa lafiya da ’yan uwansu su ba da haɗin kai, tare da bayyana cewa an samar da hanyoyin karɓar koke-koke domin inganta ayyukan lafiya.
Dakta Nagoda ya yabawa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf bisa goyon bayan da yake bai wa bangaren lafiya, musamman amincewa da sayen injinan ʼdialysisʼ domin inganta ayyukan jinya.